Yau ce Ranar Yaki da Jahilci ta Duniya

Littafin koyon karatu da rubutu
Image caption Littafin koyon karatu da rubutu

Yau ake bikin ranar yaki da jahilci ta duniya, da Majalisar Dinkin Duniya ta kebe don fadakarwa kan muhimmancin koyon rubutu da karatu.

Wasu alkaluma daga Majalisar ta Dinkin Duniya na cewa, mutane kimanin miliyan 800 ne watau kashi daya cikin biyar na dukkan jama'ar duniya, basu iya rubutu da karatu ba.

Ta kuma ce, kimanin kashi 78 cikin dari na maza daga shekaru 15 zuwa 24 a Najeriya basu iya rubutu da karatu ba, yayin da mata kuma kashi 65 bisa dari.

Bayanai kuma sun ce matsalar ta fi kamari a arewacin kasar.

Sakamakon rashin iya rubutu da karatu dai, wasu na bayyyana cewa hatta wasiku da sakonnin wayar salula dake bukatar sirri, sai sun nemi taimakon wadanda za su karanta ko kuma su rubuta musu.

Baya ga rashin la'akari da muhimmacin ilmi daga wasu mutane , a cewar masana gwamnatocin ba sa kulawa wajen kyautata harkar ilimin.