Kerry: 'Baki ya zo ɗaya a kan Syria'

Bayan ya gana da ministocin harkokin wajen kungiyar kasashen Larabawa, sakataren harkokin wajen Amurka, John Kerry, ya ce, baki ya zo daya a kan cewar, gwamnatin Syria ta wuce makadi da rawa, da ta yi amfani da makamai masu guba.

A birnin Paris Mista Kerry ya ce, harin da Amurka za ta jagoranta a kan Syria, manufarsa kawai ita ce: a tabbatar da cewa, an kiyaye dokokin kasashen duniya, game da amfani da irin wadannan makaman.

Akwai dai bambancin ra'ayi tsakanin kasashen larabawa dangane da batun duakar matakin soja akan Syria, amma kasashe irinsu Saudi Arabia da kuma Qatar suna goyon bayan kaiwa Syrian harin soja.