Birnin Tokyo zai karbi bakuncin Olympics na 2020

Mutane na murnar samun galabar da birnin Tokyo ya samu
Image caption Mutane na murnar samun galabar da birnin Tokyo ya samu

Tokyo babban birnin kasar Japan zai karbi bakuncin gasar wasan Olympic na shekara na 2020, bayan da ya kada abokan neman bakuncin nasa biranen Istanbul da Madrid.

An bayyana sakamakon birnin da zai karbi bakuncin gasar wasan ne bayan kada kuri'a a asirce da mambobin kwamitin gasar wasan Olympic na kasa da kasa IOC suka gudanar.

Sanarwar wacce shugaban kwamitin na IOC mai barin gado Jacques Rogge ya gabatar a kasar Argentina, ta haifar da farin ciki da sowa a fadin birnin na Tokyo.

Sakamakon dai ya nuna cewa birnin Tokyo ya samu kuri'u 60, kana birnin Istanbul 36, bayan da aka riga aka fitar da birnin Madrid tun a zagayen farko.

Kasar Japan ita ce aka bayyana kasa mafi cancanta a fannin zaman lafiya a kaunar harkar wasanni, kuma Tokyo babban birnin kasar shine wanda ya fi ko wane birni a duniya kwanciyar hankali.