'Yan sanda na bincike kan sace Archbishop

Image caption Archbishop Ignatius Kattey

'Yan sanda a Najeriya suna farautar 'yan bindigar da suka sace wani babban shugaban kiristocin kasar mabiya darikar Anglican wato Archbishop Ignatius Kattey.

Tun a ranar Juma'a aka sace shi tare da matarsa Beatrice a kusada gidansu dake birnin Port Harcourt na jihar Ribas.

An saki matarsa Beatrice sa'o'i kadan bayan an yi garkuwa dasu, kuma tana cikin kohin lafiya kamar yadda cocinsu ya bayyana.

Satar mutane don kudin fansa ya zama tamkar kasuwanci a yankin Naija Delta na Najeriya.

Kungiyar Kiristoci ta kasar CAN ta ce ta yi matukar girgiza da samun labarin sace mutum na biyu mafi girman mukami a cocin Anglican dake kasar.

Karin bayani