Sake bincike kan mutuwar Hammarskjold

Marigayi Dag Hammarskjold
Image caption Marigayi Dag Hammarskjold

Hukumar bincike ta lauyoyi da ke gudanar da bincike akan mutuwar tsohon sakatare janar na Majalisar dinkin duniya, Dag Hammarskjold ta nemi Majalisar da ta sake bude binciken.

Jirgin saman Mr Hammarskjold na kan hanyarsa ne ta zuwa kasar Congo kan aikin samar da zaman lafiya a shekarar 1961 lokacin da ya fadi a Rhodesia ta Arewa, wato kasar Zambia a yanzu.

Wakilin BBC ya ce wani bincike da Majalisar ta gudanar a shekarar 1962 ya gaza gano musabbabin mutuwar ta sa, amma dai akwai lauje a cikin nadi inda wasu kwararru ke cewa an harbi jirgin ne.

Hukumar gudanar da binciken ta ce akwai muhimman shaidu da za su taimaka a sake gudanar da binciken kuma hukumar leken asiri ta Amurka na da muhimmman bayanai kan lamarin.