Ruto ya isa kotun Hague

Image caption William Ruto zai fuskanci tuhuma kan kisan mutanen da aka yi a Kenya

Mataimakin shugaban kasar Kenya, William Ruto ya isa Hague domin fuskantar shari'a a kotun hukunta manyan laifuka ta duniya wato ICC.

Ana zargin Mista Ruto ne da shugaban kasar Kenya, Uhuru Kenyatta, da laifin kitsa tashin hankalin da ya biyo bayan zaben shugaban kasa na shekara ta 2007.

Ranar Talata ne za a fara shari'ar Mista Ruto.

Alkalai a kotun sun ce za a saurari kararrakin biyu ne a lokuta daban daban - inda za a samu makwanni hudu a tsakaninsu.

Hakan dai ya faru ne sakamakon bukatar da shugaba Kenyatta ya nema cewa bai kamata mutanen da ake karar su bar kasar ba a lokaci guda.

Karin bayani