Syria: Kerry ya gindayawa Assad sharadi

Image caption John Kerry da William Hague suna kamun kafa a kan Assad

Sakataren harkokin wajen Amurka, John Kerry ya ce za a kauda kai harin soji ne kawai a kan Syria, idan har Shugaba Assad ya mika makamansa masu guba cikin mako guda.

Mista Kerry ya bayyana haka ne a London a ziyararsa ta karshe a yinkurin neman goyon bayan don amfani da matakin soji a kan gwamnatin Syria bisa zargin amfani da makami mai guba.

A cewarsa amfani da matakin soji da Amurka za ta yi, baya nufin cewar yaki ne za a shiga a Syria amma wata hanya ce ta magance rikicin.

'Babu hujja'

Shugaban Syria Bashar al-Assad ya shaidawa wata kafar yada labarai ta Amurka cewar "babu hujja" a kan cewar gwamnatinsa ta yi amfani da makamai masu guba.

A hirarsa da PBS da aka watsa a ranar Litinin, ya ce kawayen Syria za su mayar da martani idan har kasashen yammacin duniya suka kai masa hari.

A ranar Litinin majalisar dokokin Amurka za ta koma hutu inda za ta soma mahawarar kan kudurin shugaba Obama na kaddamar da 'takaitaccen hari'.

Karin bayani