Nijar na neman agaji saboda Tamowa

Image caption Matsalar tamowa ta addabi Nijar

Hukumomin jamhuriyar Nijar sun yi kira ga kasashe masu arziki su taimaka mata domin shawo kan matsalar tamowar da ta shafi kashi 13 cikin 100 na kananan yaran kasar a wannan shekarar.

Rahoton wani bincike da gwamnatin ta yi ta kuma wallafa a karshen makon nan, ya ce duk da cewa tamowar ta yi sauki a bana ba kamar bara ba, har yanzu ta haura ma'aunin hukumar kiwon lafiya na kashi 10 cikin 100 da ake iya dauka tamkar lamarin bai tsananta ba.

Shekara da shekaru Nijar na fuskantar matsalar tamowa musamman saboda rashin kyawun damuna.

Jamhuriyar Nijar na daga cikin kasashe mafi talauci a duniya.

Karin bayani