Rasha ta nemi Assad ya mika makamansa

Masu binciken makamai na Majalisar Dinkin Duniya
Image caption Sakataren wajen Amurka, John Kerry ya baiwa Syria mako guda ta mika makamanta

Rasha ta bukaci kasar Syria ta mika makamanta masu guba 'karkashin ikon kasa da kasa' domin kauce wa matakin sojin Amurka.

Kuma za a lalata makaman ne, idan Syria ta amince ta mika su.

Rasha ta yi wannan tayin ne a wata ganawa tsakanin ministan harkokin wajenta, Sargei Lavrov da takwaransa na Syria, Walid Muallem.

Kuma Mr. Muellin ya yi maraba da tayin.

Amurka na barazanar kaiwa Syria hari, bisa zarginta da aikata laifukan yaki, zargin da Syria ta musanta.