ICC: Ruto na kan hanyarsa zuwa Hague

Image caption Mataimakin Shugaban Kenya, William Ruto

Mataimakin Shugaban Kasar Kenya, William Ruto, ya na kan hanyarsa ta zuwa birnin Hague inda zai gurfana a gaban kotun shari'ar manya manyan laifuffuka ta kasa da kasa.

Ana zargin Mr Ruto ne da kuma Shugaban kasar Kenya, Uhuru Kenyatta da laifin kitsa tashin hankalin da ya biyo bayan zaben shugaban kasa na shekara ta 2007.

A yayin da ya ke jawabi ga manema labarai, magatakardan kotun, Herman von Hebel, ya ce matsayin kotun shine ta binciko wanda ke da alhakin tashin hankalin.

Yace "na yi imanin, aikinmu ne domin tabbatar da cewar an yiwa mutane ukkun da ake zargi adalci, sannan kuma an ji ta bakin wadanda tashin hankalin ya rutsa da su".

Karin bayani