Somalia za ta sa yara miliyan 1 a makaranta

Image caption Yaran 'yan mata a makaranta

Hukumomin Somalia sun kaddamar da wani kamfen na neman sa yara miliyan guda a makarantu.

Shirin, wanda aka yi wa lakabi da: 'Ku je makaranta', zai fara ne a lokaci guda a Mogadishu, babban birnin kasar, da kuma a manyan biranen yankunan Somaliland da Puntland, tare da tallafin hukumar kula da kananan yara ta majalisar dinkin duniya, watau UNICEF.

Bayan an kwashe shekaru ashirin ana yakin basasa a kasar, UNICEF din ta ce, Somaliyar na daga cikin kasashen da ke can baya wajen sa yara makaranta.

Yara hudu daga cikin goma ne kawai ke zuwa makaranta a Somaliyar.

Shirin samar da ilimi ga kananan yara din zai lashe dala miliyan 117 a kasar ta Somalia.

Karin bayani