'Yan PDP su 7,000 sun koma APC a Zamfara

Image caption Jam'iyyar APC na da farin jini a arewacin Najeriya

A Jahar Zamfara da ke arewacin Najeriyar, wasu 'yan jam'iyyar ta PDP su kimanin 7,000 sun sauya sheka zuwa jam'iyyar APC mai mulki a jihar.

Wadanda suka canja shekar dai a wani gagarumin biki da aka shirya a Gusau babban birnin jahar, sun hada da wasu tsoffin shugabannin PDP da kuma wasu tsoffin masu rike da mukamai a tsohuwar gwamnatin jahar.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da jam'iyyar PDP ke fuskantar matsalolin cikin gida inda wasu gwamnoni suka balle.

Tun da aka koma mulkin demokradiyya a Najeriya dai, jam'iyyar PDP ce ke mulkin kasar amma a 'yan shekarunnan tana fuskantar kalubale musamman dunkulewar jam'iyyun adawa waje guda.

Karin bayani