Brazil za ta nemi bahasi kan zargin Amurka

glen greenwald
Image caption A mako mai zuwa Greenwald da Miranda za su ba da bahasi a gaban majalisar Brazil

Hukumar majalisar dokokin Brazil da ke binciken zargin leken asiri a kan Amurka ta ce za ta gayyaci Glenn Greenwald na jaridar Guardian da abokin mu'amalarsa David Miranda domin ba da bahasi.

A kwanakin nan Mr Greenwald ya buga wasu takardu da ke zargin hukumar tsaron Amurka na satar sadarwar shugabar kasar Brazil Dilma Rosseuff.

Baya ga shugabar har ma da sadarwar wasu manyan jami'an gwamnatin Brazil.

Wani rahoton ya kuma zargi Amurka da satar sanya ido a kan harkokin kamfanin mai na Brazil Petrobras.