An samu maza 4 da laifin fyade a Indiya

Motar kurkuke dake dauke da masu laifin
Image caption Lamarin ya janyo kafa dokoki masu tsauri, domin hukunta masu aikata cin zarafin mata a Indiya

Wata kotu a Indiya ta samu wasu maza hudu da laifin yin fyade, ga wata daliba a birnin Delhi a watan Disambar bara.

Lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar dalibar mai shekaru 23, makonni biyu bayan gungun matasan su yi mata fyade a cikin mota kirar bas.

Hakan ya janyo zanga-zanga a fadin kasar.

A ranar Laraba ne ake sa ran za a yanke musu hukunci, kuma akwai yiwuwar su fuskanci hukuncin kisa.

Mukesh Singh da Vinay Sharma da Akshay Thakur da Pawan Gupta sun musanta zargin yin fyaden da kuma kisa.