Yinkurin inganta ilimi a Najeriya

  • 10 Satumba 2013

Gwamnatin Najeriya tare da hadin gwiwar majalisar dinkin duniya ta yi wani taro na musamman don kafa wata gidauniya ta dala miliyan dari biyar da nufin inganta ilimi a Najeriya.

Wasu alkaluma da asusun raya ilimi na majalisar dinkin duniyar ya fitar ya nuna cewa, sama da yara miliyan goma ne ba sa karatu a kasar.

Ana sa ran cewa za a yi amfani da wannan kudi ne wajen samar da kayan karatu da inganta kwazon malamai a makarantun Najeriyar ta yadda za a samar da guraben karatu ga wadannan yara da ke gararamba.

Karin bayani