Dogaran sarkin Hadejia 11 sun mutu

Hadarin mota a Najeriya
Image caption Hadarin mota a Najeriya

Rahotanni daga jihar Jigawar Najeriya sun nuna cewa, dogarawan sarkin Hadejia kimanin 11 ne suka rasa rayukansu, a wani hadarin mota.

Rahotannin sun ce hadarin ya faru a yammacin ranar Litinin.

Dogarawan na kan hanyar su ne ta zuwa tarbar sarkin Hadejan, Alhaji Adamu Abubakar Maje, wanda ya dawo daga bulaguron da ya ya yi zuwa kasar waje.

Shaidu sun ce motar da dogarawan ke ciki ta yi taho mu gama ne da wata tankar mai, a kan hanyar Ringim zuwa Zakirai dake jihar Jigawa.