Obama ya yi jawabi a kan Syria

barack obama
Image caption ''Dole ne Amurka ta tabbatar da aiwatar da yarjeniiyoyin kasashen duniya'', in ji Obama

A wani jawabi da ya yi wa al'ummar Amurka ta talabijin daga fadar gwamnatin kasar White House shugaba Obama ya bayyana dalilansa na daukar mataki a kan gwamnatin Syria.

Gwamnatin da ya bayyana karara da cewa ita ke da alhakin amfani da makamai masu guba da suka hallaka sama da mutane dubu daya.

Mr Obama ya ce ko da ike Amurka ba 'yar sandar duniya ba ce,amma hotunan da aka nuna na amfani da guba a kan mutane abu ne mai tada hankali da ke bukatar martani.

Ya ce ya fahimci cewa mutane da dama sun gaji da yaki, to amma amfani da makamai masu guba da Syria ta yi barazana ce ga yankin da kuma tsaron Amurka.