Ana rikici a kudancin Philippines

Image caption Dakarun Phillipines

An tura karin sojoji da 'Yan sanda zuwa birnin Zambaonga dake kudancin kasar Philippines, domin katse hanzarin Musulmi 'yan tawaye da suka kwace wani bangare na birnin.

Ana ci gaba da musayar wuta, kwana na biyu a jere, bayan da wasu 'yan tawaye sama da su dari suka isa ta jiragen ruwa, suka kuma kwace wasu unguwanni na gabar teku.

'Yan bindigar na kungiyar 'yan aware ta Moro National Liberation Front, dake neman ikon cin gashin kai na Musulmi a Kudancin Philippines.

Kungiyar ba ta cikin tattaunawar da gwamnati ke yi da wasu kungiyoyin 'yan tawaye don neman sulhu.