Ruto ya musanta zargin cin zarafi a ICC

William Ruto a kotun hukunta manyan laifukan yaki na duniya
Image caption Shari'ar na da sarkakiyar siyasa a tarihi, a cewar mai aiko wa BBC rahotanni a Hegue, Anna Holligan

Mataimakin shugaban kasar Kenya, William Ruto ya musanta zargin aikata laifukan yaki, da suka danganci cin zarafin jama'a.

Mr. Ruto ya dauki wannan matsayin ne, a lokacin da ya bayyana a gaban kotun hukunta manyan laifukan yaki ta duniya, ICC a ranar Talata.

Shi ne dai mai rike da babban mukami a Afrika na farko, da ya fara gurfana a gaban kotun dake zamanta a Hague.

Mr. Ruto da shugaba Uhuru Kenyatta na fuskantar zarge-zarge, da suka shafi rikicin da ya biyo bayan zaben shugaban kasa a kenya a shekarar 2007.