Apple ya fitar da iPhone 5S da 5C

Image caption Wayar iPhone 5S da kuma 5C

Apple ya fitar da sababbin wayoyin salula biyu, iPhone 5S da kuma mai saukin kudi iPhone 5C a wani buki a Califonia na Amurka.

Wayar 5S za ta dunga amfani da hoton yatsan mai wayar. A yayinda wayar 5C keda murfin roba mai kaloli daban daban.

Fitar da wayoyin wani sauyin dabara ce ga kamfanin Apple don kiran kasuwa.

Wani masana ya bayyana cewar wadannan wayoyin za su yi goggawa da sauran abokan hamayya kirar Android.

'Ba sauki'

Image caption Sabobbin wayoyin ba suda sauki

Farashin wayar iphone 5S ya soma daga fan 549 wacce keda gigabyte 16 a yayinda wayar mai gigabyte 64 ta tashi a kan fan 709.

Sai kuma iphone 5C mai gigabyte 16 wacce za a siyar a kan fan 469 wato tafi farashin da ake sayarda 4S a Ingila.

Ben Wood mai bada shawara a kamfanin CCS Insight ya ce "wayar 5C ba tada sauki idan aka kwatanta da wayar iPhone 4S".

Akwai jita-jitar za a daina kera wayar 4S.

A ranar 20 ga watan Satumba za a soma sayar da sabobbin wayoyin iPhone a Amurka da Birtaniya da China da Australia da kuma Canada.