CAR: An kori babban hafsan sojin kasa

Image caption Dakarun 'yan tawaye na Seleka

An kori babban hafsan sojin kasa na Jamhuriyar Afrika ta tsakiya daga mukaminsa bayan da dakarun dake biyayya ga hambararren shugaban kasar suka kaddamar da hari.

Hukumomi sun ce akalla mutane 60 sun mutu sakamakon tashin hankalin da ya auku a wani birni dake arewa maso yammacin babban birnin kasar Bangui.

A farkon wannan watan aka rantsar da tsohon shugaban 'yan tawaye Michel Djotodia bayan da dakarunsa suka hambararda Francois Bozize a watan Maris.

Kashi daya cikin uku na al'ummar kasar na bukatar tallafin abinci da magani da ruwa.

Dakarun dake biyayya da Mista Bozize sun kwace akalla gari daya tun da aka soma bata kashin a makon daya wuce.

Karin bayani