PDP: Wasu gwamnoni sun kauracewa Jonathan

Image caption Batun ko Shugaba Jonathan zai yi takara a 2015 na janyo cece-kuce a jam'iyyar PDP

Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan ya gana da wasu gwamnonin jihohi 'yan bangaren 'sabuwar' PDP da ta balle daga jam'iyya mai mulkin kasar da nufin warware rikicn da ya dabaibaye jam'iyyar.

Gwamnoni hudu ne daga cikin bakwai da ke bangaren sabuwar PDP suka halarci zaman.

Sai dai babu wani cikakken bayani a kan abin da suka cimma a tattaunawar da suka yi cikin sirri inda suka kwashe kusan sa'o'i shida.

Gwamnonin jihohin Jigawa da Adamawa da Niger da kuma Sokoto ne suka halarci zaman.

Wasu majiyoyi sun ce gwamnoni 'yan bangaren sabuwar PDP sun jaddada bukatar cewa lallai sai an yi na'am da jagorancin takwararsu Gwamnan jihar Rivers Rotimi Amechi a matsayin shugaban kungiyar gwamnonin kasar, tare da sauke Alhaji Bamanga Tukur da wasu makarrabansa daga shugabancin jam'iyyar PDP.

Karin bayani