Ana dab da gano rigakafin HIV

Image caption Sakamakon binciken ya nuna cewa kimanin rabin birran da aka sa wa cutar sun warke sarai.

Masana kimiyya a Amurka sun yi gwajin wata allurar rigakafi a kan birai, kuma bisa dukkan alamu tana aiki wajen hana kamuwa da wata kwayar cuta kwatankwacin HIV.

Sakamakon binciken da aka wallafa a mujallar Nature, na nuna cewa kimanin rabin birran da aka sa wa cutar sun warke sarai.

A yanzu masana kimiyyar sun kirkiro wani nau'i na wannan allurar da za a iya gwajinsa a kan Bil'adama.

Sai dai da farko sai an yi gwaji don tabbatar da cewa ba shi da wani hadari.

Ana fatan za a fara gwajin maganin nan da shekaru biyu masu zuwa.

Karin bayani