Kotun hukunta laifukan yaki ta wanke Najeriya

Shugaba Omar El-Bashir a ziyarasa zuwa Najeriya
Image caption Ma'aikatar harkokin wajen Najeriya ce ta sanar da matsayin ICC game da kasar

Kotun hukunta manyan laifukan yaki ta duniya, ICC ta wanke Najeriya bisa rashin mika shugaban Sudan Omar Al- Bashir, a lokacin da ya je kasar.

Shugaba Al-Bashir ya je Najeriya a watan Yunin da ya gabata, domin halartar taron koli na kungiyar tarayyar Afrika.

Najeriya ta sha suka daga kungiyoyin kare hakkin dan Adam na cikin gida da kuma kasashen waje game da lamarin.

Kotun dai ta ba da sammacin kama Albashir, bisa tuhumarsa da aikata laifukan yaki a yankin Darfur.