'Yan sanda za su yi rajistar ababen hawa

Supeton Yansandan nijeriya
Image caption Yansandan nijeriya za su fara rajistar ababen hawa

A Najeriya rundunar 'yan sandan kasar ta ce za ta fara yin wata sabuwar rajistar ababen hawa da nufin inganta aikinta na hana aikata laifuka da yaki da ta'addanci.

Rundunar ta ce za ta fara aikin gudanar da rajistar a duk fadin kasar daga ranar goma sha shida ga watannan da muke ciki na Satumba.

To sai dai tuni wasu masu ababen hawa suka fara korafi game da wannan yunkuri.

Sai dai wasu 'yan majalisar kasar na cewa akwai yiwuwar su duba lamarin, idan har jama'a na cigaba da korafi.