Obama ya sauya matsayi a kan Syria

Shugaba Obama na Amurka
Image caption Obama ya ce zai dauki matakin soji kan Syria idan diplomasiyya ta ci tura

Shugaban Amurka Barack Obama ya ce gwamnatinsa ta jingine batun daukar matakin soji kan Syria, domin mayar da hankali kan matakan diplomasiyya kamar yadda Rasha ta kawo shawara.

A wani jawabi da ya yi wa al'ummar Amurka ta talabijin, shugaba Obama ya jaddada cewa muddin matakan diplomasiyyar suka ci tura, to kuwa ba makawa, Amurka za ta dauki takaitaccen matakin soji a kan Syria..

Gwamnatin da ya bayyana karara da cewa ita ce ke da alhakin amfani da makamai masu guba da suka hallaka sama da mutane dubu daya.

Mr Obama ya ce kodayake Amurka ba 'yar sandar duniya ba ce, amma hotunan da aka nuna na amfani da guba a kan mutane abu ne mai tada hankali da ke bukatar martani.

Obama ya ce kusan shekaru 70 Amurka ta kasance jagaba wajen tabbatar da tsaro a duniya, hakan kuma ba wai kawai ya tsaya ga tabbatar da yarjejeniyoyin kasashen duniya ba ne kawai har da tilasta aiwatar da su.

Yace ya fahimci cewa mutane da dama sun gaji da yaki, to amma amfani da makamai masu guba da Syria ta yi barazana ce ga yankin da kuma tsaron Amurka.