Ana faman gumurzu a garin Ma'alula na Syria

Maaloula

An gwabza kazamin fada a garin Ma'alula na Syria, wanda gari ne mai dimbin tarihi na Kristoci.

Rahotanni na cewa dakarun gwamnati sun kwace shi daga ikon masu kaifin kishin Islama da ke tawaye.

Wakilin BBC da ya je garin na Ma'alula ya ce, cikin kimanin rabin sa'a da ya wuce, ya ji karar mummunar musayar wuta, da kuma kara mai karfi ta fashewar wasu abubuwa.

Ya kuma ce dakarun gwamnatin Syria sun kwace iko da tsakiyar garin.

Wakilin namu ya kara da cewa bai ga wani wuri, ko alama ta ibada da 'yan tawayen suka lalata ba, sabanin rahotanin da ke cewa sun kai hari kan wasu wuraren tarihi na Kiristoci.

Ma'alula na da muhimmin tarihi a Syria, har yanzu wasu mazauna garin suna amfani da harshen Aramaic, ko Al Aramiyya, harshen da ake amfani da shi a zamanin Annabi Isa Alaihis Salam.