Duka bangarorin rikicin Syria na da laifi

Image caption An lalata galibin kasar Syria

Rahoton Majalisar Dinkin Duniya na baya baya kan kare hakin bil adama a Syria ya ce dukkan bangarorin rikicin kasar sun aikata laifukkan yaki da cin zarafin bil-adama.

Rahoton ya ce azabtarwa da kuma aikata fyade sun zamo ruwan dare, kuma dakarun gwamnati sun yi amfani da bama bamai masu kwanso a wurare da dama.

Rahoton ya ce 'yan adawa na ci gaba da aikata kisan gilla a kan jama'a.

Jami'an bincike na Majalisar Dinkin Duniya da suka wallafa rahoton sun ce suna da jerin sunaye na mutanen da aka hakikance sun aikata laifukan yaki, kuma wajibi ne a gurfanar da su a gaban kotu.

Kasar China ta buka ayi taka tsantsan kan batun Syriar.

'Amurka'

Shugaban Amurka Barack Obama ya ce gwamnatinsa ta jingine batun daukar matakin soji kan Syria, domin mayar da hankali kan matakan diplomasiyya kamar yadda Rasha ta kawo shawara.

A wani jawabi da ya yi wa al'ummar Amurka ta talabijin, shugaba Obama ya jaddada cewa muddin matakan diplomasiyyar suka ci tura, to kuwa ba makawa, Amurka za ta dauki takaitaccen matakin soji a kan Syria..

Gwamnatin da ya bayyana karara da cewa ita ce ke da alhakin amfani da makamai masu guba da suka hallaka sama da mutane dubu daya.

Karin bayani