'Yan bindiga sun kashe 'yan sanda a Adamawa

Sojojin Najeriya
Image caption Adamawa na daga cikin jihohi uku da gwamnatin Najeriya ta sanya wa dokar-ta-baci

A jihar Adamawa a Najeriya, an kashe jami'an 'yan-sanda biyu tare da jikkata wani jami'in guda, a wani harin da wasu 'yan bindiga suka kai.

Maharan da ba a san ko su wanene ba, sun kona ofishin 'yan sanda dake garin Ga'anda, dake karamar hukumar Gombi a jihar.

Hukumomin tsaro a jihar sun ce 'yan bindigan sun shiga garin ne a motoci da babura, kuma suka yi amfani da mugayen makamai wajen yin artabu da jami'an tsaro.

Rundunar 'yan sandan jihar ta ce tana bincike a kan al'amarin da ya auku a ranar Laraba da daddare.