Koriya ta Arewa ta dawo da aikin nukiliya

wurin aikin nukiliyar korea ta arewa
Image caption Amurka ta nanata kira ga Korea ta Arewa ta kiyaye da yarjejeniyar dakatar da aikinta na nukiliya

Wasu hotunan tauraron dan adam na ma'aikatar nukiliya ta Yongbyon sun nuna alamun cewa Korea ta Arewa ta dawo da aikinta na nukiliya.

Masana a cibiyar bincike ta Amurka da Korea sun ce wani hoto da aka dauka ranar 31 ga watan Agusta ya nuna wani tarin farin hayaki yana bulbulowa daga wani gini inda na'urorin hada makamashin nukiliyar Korea ta arewan su ke.

Masanan suka ce yawa da kuma launin hayakin alamu ne da ke nuna cewa cibiyar na aiki ko kuma tana gab da fara aiki.

A watan Afrilu Korea ta Arewa ta ce ta shirya dawo da aikin cibiyar wadda za ta iya samar da kilogram shida na sanadarin nukiliya na plutonium a shekara daya.