Assad ya mika wuya game da makamai

Image caption Magoya bayan Shugaba Assad

Shugaban Syria Bashar al-Assad ya bayyana a gaban gidan talabijin na Rasha inda ya tabbatar da cewar kasarsa za ta mika makamanta masu guba karkashin kulawar kasa da kasa.

Mista Assad ya shaidawa tashar Rossiya 24 ya dauki matakinne sakamakon shawarar Rasha amma ba barazanar daukar matakin soji da Amurka tayi musu ba.

Kalamansa na zuwa ne a daidai lokacin da ministocin harkokin wajen Rasha da Amurka ke shirin soma wata tattaunawa a Geneva.

Amurka na zargin gwamnatin Syria da kashe daruruwan mutane da sinadari mai guba a wani hari a Damascus a ranar 21 ga watan Agusta.

Gwamnatin ta karyata zargin, inda tace 'yan tawaye ne suka kai harin.

'Jan kunne'

Shugaban Rasha Vladimir Putin ya gabatar da wani sako ga al'ummar Amurka a kan Syria.

A wani sharhi da ya rubuta a jaridar New York Times, Putin ya yi gargadin cewa duk wani hari da Amurka za ta kai wa Syria, zai bude wani sabon babi ne na hare-haren ta'addanci, kuma zai iya gurgunta dokokin duniya.

Mr. Putin ya kuma soki Amurka da cewa mutane da dama fa a duniya, ba sa kallonta a matsayin abar koyi a tsarin dumokradiyya, illa kasar da ta dogara da amfani da karfin tuwo.