Kerry da Lavrov na tattaunawa kan Syria

John Kerry da Sergei Lavrov
Image caption John Kerry da Sergei Lavrov

Sakataren harkokin wajen Amurka, John Kerry, da takwaran aikinsa na kasar Rasha, Sergei Lavrov, sun yi magana akan bukatar warware rikicin makamai masu guba na Syria, gabanin taron da za'a yi a Geneva.

Mr Kerry ya ce duniya ta zuba ido ta ga ko gwamnatin Assad zata cika alkawarin ta a kan makamai masu guba ko kuma a'a.

Ya ce kalaman da shugaban ya yi basu isa ba.

A nashi bangaren Mr Lavrov ya ce tilas ne a samu hanyar da za'a kaucewa fito na fito na soji.

Ya ce kudurin doka kan batun makamai masu guba na Syria zai hana daukar kowane matakin soji da Amurka ke kokarin yi.

Majalisar Dinkin Duniya ta sami wasika daga gwamnatin Syria, inda take bayyana aniyarta ta shiga yarjejeniyar kasa da kasa dake sa ido akan makamai masu guba.

Kasar Syria na daga cikin kasashe biyar da basu riga sun sa hannu kan yarjejeniyar makamai masu guba ba, wadda ta hana kerasu, ajiyesu da kuma amfani da su.

A wata hira da ya yi da gidan talabijin na kasar Rasha, Shugaba Assad ya ce Syria zata fara mika bayananta akan makamai masu guba ga kungiyar bayan kwanaki talatin, kamar yadda yarjejeniyar ta tanada.

Shugaba Assad ya ce Rasha ita kadai ce kasar da zata sa wannan yarjejeniya ta yi aiki, ganin cewa Syria bata da wata hanya ta tuntubar Amurka.

Sai dai kuma sakataren harkokin wajen Amurka, John Kerry, ya yi watsi da hakan, yana mai cewa bin ka'ida bashi da amfani bayan an riga an yi amfani da makamai masu gubar.