An kama fasto zai kona Qur'anai a Amurka

Fasto Terry Jones a motar da aka kama shi
Image caption Fasto Terry Jones

'Yan sanda a Florida ta Amurka sun cafke wani fasto wanda ke shirin kona Alkur'ani mai tsarki kusan dubu uku.

Faston Terry Jones na dauke da Qur'anan da ya zuba wa kalanzir a wata babbar motar da yake tukawa.

Yace ya yi niyyar kona kowanne kur'ani a madadin kowane mutum guda da ya mutu a harin 11 ga watan Satumba, shekaru 12 da suka wuce.

'Yan sanda sun ce ana tuhumarsa da wasu mutane a kan daukar man fetur ba bisa ka'ida ba.

Jones wanda ke jagorantar wani karamin coci na darikar evangelica a Amurka, ya taba barazanar kona kur'ani a shekarar 2010.

Haka kuma ya sha jagorantar zanga-zangar kin jinin musulmi, yayin da mutanen mujami'arsa suka taba kona kur'ani a shekarar 2011.