An kara kudin shiga motar haya a Ghana

Image caption Motar haya a Ghana

A kasar Ghana kungiyar masu motocin haya ta yi karin kashi ashirin cikin dari na kudin shiga mota a dukkan fadin kasar daga Asabar.

Kungiyar ta ce ta dauki wannan matakin ne saboda karin farashin man fetur da gwamnati ta yi har so uku, a watannin baya.

Sai dai tun kafin lokacin, wasu direbobi sun fara karbar sabon farashin.

Galibin al'ummar Ghana suna zirga-zirga ne a cikin motocin haya.