An zalunci mutane wajen korarsu a Somalia

Image caption Matsalar tamowa a wani sansani a Mogadishu

Kungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty International ta yi Allawadai da yadda aka kori dubban mutanen da suka rasa muhalinsu daga sansanin da aka tsugunar da su na wucin gadi a Mogadishu babban birnin Somalia.

Kungiyar ta ce yayin korar tasu an kashe mutane biyu ta kuma yi zargin cewa an ci zarafin da dama daga cikin mutanen.

'Yan gudun hijira dubu 370 ne suka samu mafaka a birnin bayan da suka tsere wa fada a garuruwansu.

Zamansu a sansanonin ya kawo cikas ga shirin gwamnati na sake gina birnin na Mogadishu, kasancewar an kori mayakan kungiyar Al-Shabab.

Hukumomin kasar sun yi shirin tsugunar da dubban 'yan gudun hijirar a wasu sabbin sansanoni uku a wajen birnin, amma fargaba kan tsaro ta sa aka dakatar da daya daga cikinsu.

Karin bayani