Ana samun ci gaba a ganawar Kerry da Lavrov

Image caption John Kerry da Sergie Lavrov

Sakataren harkokin wajen Amurka, John Kerry, da takwaransa na Rasha, Sergei Lavrov sun ce tattaunawarsu a kan karbe makamai masu guba daga hannu gwamnatin Syria matakin farko ne na wani babban shiri na kawo karshen rikicin kasar.

A rana ta biyu ta tattaunawarsu a Geneva, hadda wakili na musamman na Majalisar Dinkin Duniya kan Syria, Lakhdar Brahimi, Mr Kerry ya ce ana samun ci gaba a tattaunawarsu yayin da suke kokarin lalubo matsaya guda.

Mr Lavrov ya ce za su kara yin wani taron a wajan babban taron Majalisar Dinkin Duniya da za a yi nan gaba a wannan wata a New York, inda za su tattauna kan shirye-shiryen gudanar da wani taron kawo zaman lafiya a Syria.

'Kulawa'

Masu bincike kan take hakkin bil adama na Majalisar Dinkin Duniya sun ce dakarun gwamnatin Syria na hana mutanan dake wuraren da ke hannu 'yan adawa damar samun kulawa daga ma'aikatan jinya.

A cikin rahotansu na baya bayannan, tawagar masu binciken ta ce dakarun Syrian na kai hari kan asibitoci, suna kai hari ta sama kan asibitocin wucin gadin da aka kafa a filaye kuma suna kaiwa ma'aikatan lafiya hari.

Karin bayani