Amurka da Rasha sun gana kan Syria

John Kerry da Sergie Lavrov
Image caption Sakataren harkokin wajen Amurka da takwaransa na Rasha sun gana a kan batun makaman Syria masu guba

Jami'an Amurka sun ce sakataren harkokin wajen kasar, John Kerry da takwaransa na Rasha Sergei Lavrov sun yi ganawa ta farko, kan yadda za a mayar da makaman Syria masu guba karkashin kulawar kasashen duniya.

Kafin zaman Mr Kerry, ya ce duniya ta zuba ido ta ga ko gwamnatin Assad za ta martaba alkawarinta na mika makamanta masu guba.

Shi kuwa Mr. Lavrov ya ce lalle ne a kauce wa duk wata barazana ta amfani da karfi a kan batun.

Jami'an biyu dai za su sake ganawa a ranar Juma'a tare da wakilin musamman na Majalisar Dunkin Duniya, Lakhdar Brahimi.

Karin bayani