Mutuwar yara bai ragu ba a Najeriya - UNICEF

Tambarin asusun UNICEF
Image caption Rahoton an fitar da shi ne da hadin gwiwar babbn bankin Duniya da kuma hukumar lafiya ta duniya

Wani rahoto da asusun tallafawa yara na majalisar dinkin duniya, UNICef ya fitar a ranar juma'a, game da mace-macen kananan yara ya ragu zuwa rabi daga shekarar 1990.

Sai dai kimanin yara sama da miliyan shida ne suka mutu a bara, kuma kusan rabinsu sun fito ne daga kasashe biyar wato Najeriya da Congo da India da Pakistan da kuma China.

Abin da ke nufin akwai bukatar kasashe irinsu Najeriya su kara shan damara, wajen magance matsalar.

Rahoton yace ba a samu wani sauyi ba game da yawan yara 'yan kasa da shekaru biyar, dake mutuwa a tsakiya da yammacin Afrika.