Mutane fiye da 20 sun mutu a harin bom a Iraqi

Harin bom a kasar Iraqi
Image caption Harin bom a kasar Iraqi

Yansanda a kasar Iraqi sun ce wani dan harin kunar bakin wake a birnin Mosul dake a arewacin kasar ya hallaka mutane fiye da ashirin.

Lamarin ya abku a lokacin jana'izar wani dan karamar kabilar Shabak.

Mutane da dama ne kuma suka samu munanan raunuka sakamakon harin.

Rahotanni sun ce babu tabbaci kan ko su waye ke da alhakin kai harin, amma a baya 'yan kungiyar Sunni sun sha kaiwa kabilun na Shabak da galibin su 'yan Shi'a ne hari.

A ranar Juma'ar da ta gabata ne dai mutane talatin suka hallaka, bayan da wasu bama bamai biyu suka tashi kusa da masallacin 'yan Sunni a garin Baquba dake arewacin birnin Bagadaza.