Mahaukaciyar guguwa a kasar Mexico

Mahaukaciyar guguwar Ingrid a kasar Mexico
Image caption Mahaukaciyar guguwar Ingrid a kasar Mexico

Kasar Mexico na fuskantar bala'in mahaukaciyar guguwa a kan gabar yammaci da kuma Gabashin Kasar.

An kwashe fiye da mutane 25,000 daga gidajensu gabanin wata mahaukaciyar guguwa da Hurricane Ingrid wacce tuni ke gudun kilomita dari da ashirin cikin sa'a guda.

Ana kuma tsammanin za 'a ji tasirin karfin iskar a 'yan kwanaki masu zuwa

Tuni dai wata guguwar ta tunkari gabar tekun yammacin Kasar akan tekun Pacific, tare da ruwan sama mai karfi ninkin abinda ake gani a wata cikin kwanki uku kachal a jahohin Oxaca da Guerrero da kuma Chihuahua