Ana ta gwabza fada a kudancin Philippines

Sojojin gwamnatin Philippines
Image caption Sojojin gwamnatin Philippines

Gwamnatin Philippines ta ce, dakarunta na kokarin sake karbe unguwannin da 'yan tawaye Musulmi suka kwace a wani birni da ke kudancin kasar.

Shugaban kasar, Benigno Aquino, da mataimakinsa sun je birnin na Zamboanga mai tashar jiragen ruwa, don kokarin kawo karshen fito-na-fiton da sojoji suka kwashe mako guda suna yi da kungiyar kwatar 'yancin kai ta 'yan kabilar Moro, wadda mayakanta suka yi garkuwa da mutane dayawa.

Shugaba Aquino ya ce gwamnatinsa bata ga zama ba har sai ta shawo kan lamarin kuma tana da isassun dakaru.

An ce fiye da mutane hamsin sun hallaka a fadan da ake.

'Yan tawayen sun fito daga kungiya daya ce kawai daga cikin kungiyoyi da daman da suka kwashe shekaru dayawa suna yakar gwamnatin ta Philippines.