mutane biyu sun halaka a Rwanda

Rwanda
Image caption Rwanda

'Yan sanda a Rwanda sun ce mutane biyu sun hallaka, yayin fashewar bama-bamai a Kigali, babban birnin kasar.

A cewar jami'an tsaron, jiya da dare gurneti daya ya fashe a wata kasuwa da ta cika makil.

Mutum daya ya mutu a nan, sannan wasu goma sha hudu suka jikkata.

A yau asabar kuma wani mutumin ya hallaka, kana wasu takwas sun sami raunuka, yayin fashewar wani gurnetin.

'Yan sandan suka ce an kama mutane uku dangane da lamarin.

A ranar Litinin mai zuwa ake shirin gudanar da zaben majalisar dokoki a Rwandar.

Tun shekara ta dubu biyu da goma ne kasar ke fama da hare-haren bam, wadanda hukumomi suka dora alhakinsu a kan 'yan siyasa na bangaren adawa.