Obama ya yi maraba da yarjejeniya kan Syria

Shugaban Amurka Barack Obama
Image caption Shugaban Amurka Barack Obama

Shugaba Barack Obama na Amurka ya yi maraba da yarjejeniyar da aka cimma a Geneva kan lalata makamai masu guba na kasar Syria.

Sai dai ya yi gargadin cewa idan har aka kasa cimma nasara ta fuskar diplomasiyya, a shirye Amurka take ta dauki mataki.

Bayan tattaunawar kwanaki uku da takwaran aikinsa na Rasha a birnin Geneva, sakataren harkokin wajen Amurka, John Kerry, ya ce dole nan da mako guda Syria ta mika jerin sunayen dukkan makamai masu gubar da ta mallaka,ta kuma mika su nan da watan Nuwamba.

Mr Kerry ya ce burin da ake bukata shine na a lalata daukacin makamai masu gubar na kasar ta Syria nan da tsakiyar shekara ta 2014.

A nasa bangaren ministan harkokin wajen Rasha, Sergei Lavrov, ya ce, yarjajeniyar ko kadan bata tabo batun yin amfani da karfin soja a kan Syriar ba idan har ta ki yin biyaya.

Mr Lavrov ya ce Idan har ta kasance ba a aiwatar da wadannan bukatu ba, ko kuma wani ya sake amfani da makamai masu guba, kwamitin tsaro zai dauki kawararan matakai karkashin makala ta 7 ta dokar Majalisar Dinkin Duniya.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki-moon ya ce yana fatan yarjajeniyar za ta taimaka wajen kulla babbar yarjajeniyar kawo zaman lafiya.