An samu cigaba a tattaunawa kan batun Syria

John Kerry da Sergei Lavrov da Lakhdar Brahimi
Image caption Tattaunawa kan makamai masu guba na Syria a Geneva tsakanin John Kerry da Sergei Lavrov da Lkhdar Brahimi

Za a shiga rana ta ukku ta tattaunawar da ake yi a birnin Geneva da nufin cimma yarjejeniya a kan yadda za a kididdige da lalata makamai masu guba na Syria.

Jami'an Amurka sun ce tattaunawar na da wahalar gaske, to amma ana samun cigaba.

Wakilin BBC ya ce bayan shafe kwanaki biyu ana tattaunawar ga alama ana gab da cimma yarjejeniya dangane da yadda za a warware batun makaman masu guba na Syria.

Ana dai sa ran Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry da takwaransa na Rasha Sergei Lavrov za su yi wata ganawar ta karshe kafin su yi shelar hadin-gwiwa inda za su bayyana ka'idoji da sigogin shirin lalata makaman.

Bangarorin biyu dai suna da sauran bambance-bambance masu tsauri da za su warware, ba za a kuma tantance ba har sai sun kammala tattaunawar a kan ko an rage wasu batutuwan ko kuma an warware dukkansu.

Wata alama mai muhimmanci a cigaban da suka samu a cewar jami'an na Amurka, ita ce yadda bangarorin biyu suka kawar da jayayyar da suke yi wajen takaita yawan makaman masu guba na Syria.

Idan suka cimma yarjejeniya, Mr Kerry zai yi wa Ministocin harkokin wajen Brittaniya da Faransa bayanin tattaunawar ta su a wani taro da za su yi birnin Paris a ranar litinin.

Ana kuma sa ran za su tattauna batun da Ministan harkokin wajen Saudiyya.

Karin bayani