Amurka da Rasha sun amince da yarjejeniyar makaman Syria

John Kerry da Sergei Lavrov
Image caption Amurka da Rasha sun kammala tattaunawar Geneva

Amirka da Rasha sun amince da wani shiri da ya kunshi abubuwa shidda na kawar da makamai masu guba na Syria, tare da lalata su ba tare da bata lokaci ba, idan yin hakan ba ya tare da hadari.

Bayan tattaunawar da yayi da takwaran aikinsa na Rasha a birnin Geneva, sakataren harkokin wajen Amirka, John Kerry, ya ce dole nan da mako guda Syria ta mika jerin sunayen dukan makamai masu gubar da ta mallaka, sannan kuma nan da watan Nuwamba, ta kyale masu bincike su ziyarci wuraren.

Mista Kerry ya ce, manufa ita ce: a lalata dukan makaman Syriar masu guba nan da tsakiyar shekara mai zuwa.

A nasa bangaren ministan harkokin wajen Rasha, Sergei Lavrov, ya ce, yarjajeniyar ko kadan bata tabo batun yin amfani da karfin soja a kan Syriar ba, idan har ta ki yin biyaya.

Jami'an diplomasiyyar biyu sun kuma ce, suna son shirya taron kawo zaman lafiya da zai hada dukan bangarorin da ke da hannu a yakin basasar Syriar.

Kwamandan daya daga cikin manyan kungiyoyin tawayen Syriar, Janar Selim Idris, na Free Syrian Army, yayi watsi da yarjajeniyar da aka kulla a kan makamai masu guba na Syriar.

Ya ce, ba zata warware matsalar kasar ba, kuma zata sa Shugaba Assad ya tsira daga tuhumar kashe daruruwan fararen hula.

Sakataren majalisar dinkin duniya, Ban Ki-moon, ya ce yana fatan yarjajeniyar za ta taimaka wajen kulla babbar yarjajeniyar kawo zaman lafiya.

Shugaba Obama ya yi marhabun da yarjajeniyar da aka kulla a Geneva kan Syriar, to amma kuma yayi gargadin cewa, idan ba a sami nasara a fagen diplomasiyya ba, to Amirka a shirye take ta dauki mataki.