Hukuncin kisa kan malami a Bangladesh

AbdulQader Mollah
Image caption AbdulQader Mollah

Kotun Kolin Bangladesh ta yanke wa dan siyasar nan mai kishin Islama hukuncin kisa, bayan samun shi da aikata laifin kisan kai.

An dai tuhumi Abdul Kadir Mollah dan jam'iyyar adawa ta Jama'atul islami da kashe mutane, a lokacin yakin neman 'yancin kan kasar daga Pakistan a shekarar 1971.

An yanke masa hukuncin daurin rai da rai ne a wata kotun saurarar kararrakin yaki ta musamman, a watan Fabrariru, inda ya daukaka kara.

Lauyan dake kare shi yace wannan ne karon farko da aka maida hukuncin daurin rai da rai zuwa na kisa.

Hukunci na farko dai ya janyo zanga-zanga a kan titunan kasar.