Ronaldo ya sabunta yarjejeniyarsa

Image caption Cristiano Ronaldo

Cristiano Ronaldo ya ce yanason ya ci gaba kasancewa a Real Madrid har ya kamalla taka leda a rayuwarsa.

Ya bayyana haka ne lokacin da ya sabunta yarjejeniyarsa da kulob din har zuwa shekara ta 2018.

Dan kwallon Portugal mai shekaru 28, a lokacin ake kasuwar musayar 'yan kwallon a zaci zai koma Manchester United.

Ronaldo yace "Manchester United ta zama tarihi, yanzu Real Madrid ne gida na anan kuma zan yi ritaya"

Rahotanni daga kafafen yada labarai a Spain sun ce zai karbi albashi a duk shekara kusan Euro miliyan 17.

Ya koma Real daga Manchester United a shekara ta 2009 a kan fan miliyan tamanin 80.

Karin bayani