An bude taro kan noman kashu a Ghana

Kashu
Image caption Najeriya ma za ta yi bikin noman kashu a gobe Talata

Manoma da 'yan kasuwa daga kasashe daban-daban na duniya za su hallara a birnin Accra na Ghana, domin taro a kan noman kashu.

Manufar taron ita ce baiwa manoman kashu da kwararru tare da 'yan kasuwa, damar musayar ra'ayi kan hanyoyin bunkasa noman da kuma sarrafa kashu a duniya.

Taron na fatan za a samu bunkasar kasuwar kashu a nahiyar Afrika a nan gaba, wanda zai kara baiwa manomansa da 'yan kasuwa samun karin kudaden shiga a nahiyar .

Najeriya na daga cikin kasashen Afrikan dake noman kashu, sai dai rashin samun hanyoyin sarrafa 'ya'yan itacen, na daga cikin manyan kalubalen da manoman kasar ke fuskanta.