An fara bayar da shaida kan Ruto a ICC

William Ruto, mataimakin shugaban kasar Kenya
Image caption William Ruto, mataimakin shugaban kasar Kenya

Shaida na farko da mai shigar da kara ya gabatar ya fara ba da shaida, a shari'ar mataimakin shugaban Kenya, William Ruto.

Kotun hukunta manyan laifukan yaki ta duniya ICC, na tuhumar Mr. Ruto da wani dan jarida Joshua arap Sang da kitsa tashin hankalin da ya biyo bayan zaben shekarar 2007.

Mr Ruto dai ya musanta dukkannin tuhumar da ake yi masa.

Shirye-shiryen masu gabatar da karar dai ya gamu da cikas daban-daban, bayan da manyan masu bada shaida sun janye daga batun sauraron karar.

Mai bayar da shaidar abinda kotun ta ICC ta ce, za ta bayar da cikakkun bayanai kan yadda aka tsara kai hare-hare da kone-konen mujami'u, da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane fiye da 30, yayin barkewar rikicin bayan zaben shekara ta 2008.