Jonathan ya gana da gwamnonin sabuwar PDP

Alamar Jam'iyar PDP a Najeriya
Image caption Alamar Jam'iyar PDP a Najeriya

Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan ya gana da gwamnonin sabuwar PDP da suka balle, a ci gaba da tattaunawar sulhu.

An yi ganawar a ranar lahadi da daddare, da nufin dinke barakar dake cikin jam'iyyar PDP mai mulkin Najeriyar wacce ta rabu gida biyu.

Masu ruwa da tsaki da kuma gwamnonin Adamawa da Niger da Rivers da Kwara da Sokoto da Jigawa da Akwa Ibom da Kogi da Kano da kuma Cross River ne suka gana da shugaban Kasan da kuma mataimakinsa.

Gwamnan Jahar Niger Mua'zu Babangida Aliyu, daya daga cikin gwamnonin da suka balle, yace taron nasu ya amince kowanne bangare ya maida wukar sa .

Za a cigaba da ganawar a ranar 7 ga watan Oktoba.